Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wata cuta ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 8 a garin Dungurawa a Kano

Published

on

Wata cuta da har kawo yanzu ba a kai ga gane kowace iri ba ce ta yi sanadiyyar mutane 8 a garin Dungurawa da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar Kano.

Cutar wadda mutanen kauyen suka ce tana farawa da zazzabi mai zafi da ciwon kai ta fara ne tun kwanaki takwas da suka gabata.

Mutane takwas din da suka rasu sun hada kananan yara biyar da kuma wasu matasa su uku da shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 25.

Suleiman Musa Tafida da ya rasa ‘ya’yansa 3 ya bayyana cewa dukkan su sun fara ne da zazzabi mai zafi da ciwon kai inda bayan kaisu asibiti ana tsaka da gudanar da bincike 2 daga ciki suka rasu sai kuma yarinya daya da ta rasu a Litinin din da ta gabata.

Shi kuwa Malam Haruna Abdullahi da ya rasa dansa mai shekaru 13 ya ce dan nasa ya rasu ne akan hanyar kai shi asibiti bayan ya shafe kwanaki 2 da ya yi yana fama da zazzabi mai zafi.

Ko da muka tuntubi mai Unguwar yankin, Malam Dahiru kan lamarin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ce ya sanar da sashen lafiya na karamar hukumar Dawakin Tofa kuma jami’an lafiyar karamar hukumar sun ziyarci garin tare da fara gwaje-gwaje ga yaran yankin don gano ko akwai wata bakuwar cuta a yankin.

Freedom Rediyo ta ziyarci shalkwatar karamar hukumar Dawakin-Tofa don jin bahasin jam’ianta kan lamarin, inda babban jami’in sashen lafiya na karamar hukumar, wanda bai yarda mu nadi muryarsa ba ya ce sun samu rahoton bullar cutar.

Ya kara da cewa tuni ma har sun tura jami’ai don gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kara da cewa yanzu haka sun karbi katinan asibitin da aka rika kai wdanda suka kamu da cutar don kara zurfafa bincike.

Sai da a Talatar nan ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tura tawagar jami’anta don gudanar da bincike kan cutar ta hanyar gwajin jini da bahayar mazauna yankin

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!