Labarai
wata zanga-zanga ta kaure a kofar gidan gwamnatin Nijeriya a birnin London
Wata zanga-zanga ta kaure a kofar gidan gwamnatin Najeriya da ke Birnin London inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zaune a halin yanzu.
Sai dai da take maida martani kan zanga-zangar fadar gwamnatin tarayya ta ce barayin gwamnatin sune suka kitsa zanga-zangar.
A cewar masu zanga-zangar za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar har a kofar zauren kungiyar Commonwealth da shugaban kasar zai halarci zamanta a sati mai zuwa
A cewar masu zanga-zangar, na zargin shugaban kasar ne kan kasa magance matsalar rikicin Fulani makiyaya da manoma, tare da kasa samarwa da al’ummar kasar nan ababen more rayuwa.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa kan kafafen yada labarai malaman Garba Shehu ya ce wannan zanga-zanga bazata dauke hankalin shugaban kasar kan abin da ya kai shi birnin na London.
Haka kuma wani daga cikin yan tawagar shugaban kasar da yaki yadda a bayyana sunan sa ya ce zanga-zangar wani bangare ne na yakar gwamnati da masu cin hanci da rashawa ke yi.