Labaran Wasanni
Ya aka yi babu dan Najeriya cikin ‘yan wasa 11 da su kafi iya kwallo a Afrika?
Daga Abubakar Tijjani Rabiu
A jiya Talata bakwai ga watan Junairun shekarar 2020 hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta fitar da sunayen ‘yan wasan goma sha daya da su kafi iya murza kwallo a shekarar 2019 da ta gabata.
Sai dai cikin ‘yan wasan goma sha daya da aka fitar da babu sunan dan Najeriya ko daya a ciki, wanda hakan ya sanya masu bibiyar harkokin wasanni ke bayyana mabanbanta ra’ayoyi game da sunayen ‘yan wasan da aka fitar.
Wasu na ganin cewa hakan nada nasaba da rashin tabuka abin azo a gani da ‘yan wasan Najeriya basa yi a kungiyoyin suke wakilta musamman ma a nahiyar turai.
Za a tabbatar da hakan idan aka kalli yadda dan Sadio Mane da Riyad Mahraz da kuma Muhammad Salah ken una bajinta a kungiyoyin da suke taka leda musamman ma irin rawa da suka taka a gasar cin zakarun nahiyar turai.
A yayin da wasu ke cewa, ya kamata ace hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta sanya wasu ‘yan Nijeriya cikin jerin ‘yan wasan da suka fi iya taka leda a shekarar 2019 duba da yadda Najeriya ta kai matakin wasan dab dana karshe a gasar cin kofin Afrika na shekarar.
Haka kuma dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo shine ya ya samu nasarar lashe kyautar dan wasan da yafi kowa zura kwallo a gasar ta cin kofin Afrika inda yake da kwallaye biyar. Amma duk da wannan bajinta Ighalo bai samu damar shiga cikin jerin ‘yan wasa sha daya ba.
Samuel Chikweze dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Villareal dake kasar Spaniya shima ya nuna bajinta a kungiyar sa sannan ya taka rawar gani a gasar cin kofin Afrika. Shima dai Victor Oshimhen dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Lille a kasar France ya cancanci shiga cikin jerin ‘yan wasan duba da irin gudunmawar da ya baiwa kungiyar sa a shekarar da ta gabata.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan da hukumar kwallon kafar ta Afrika CAF ta fitar da sukafi iya murza kwallo a shekarar data gabata.
Andre Onana daga kasar Cameron dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Ajex a kasar Netherland shi ne aka zaba a matsayin mai tsaran ragar da yafi kwarewa a Afrika.
Sai masu tsaron baya wanda suka hada da Achraf Hakimi daga kasar Morocco dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da Serge Aurier dan kasar Ivory Coast dake wasa a kungiyar kwallon kafa Tottenham sai Joel Matip daga kasar Cameroon dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Kalidou Koulibaly daga kasar Senegal dake wasa a kungiyar Napoli.
Daga bangaren ‘yan wasan tsakiya kuwa an zabi Idrissa Gueye daga kasar Senegal dake wasa a kungiyar kwallon kafar Paris Saint-Germain da Riyad Mahrez daga kasar Algeria dake wasa a kungiyar Manchester City da kuma Hakim Ziyech daga kasar Morroco dake wasa a kungiyar Ajax dake kasar Netherland.
Daga bangaren masu wasa a gaba kuwa an zabi Mohamed Salah daga kasar Masar dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Sadio Mane daga kasar Senegal shima dake daga Liverpool sai kuma Pierre-Emerick Aubameyang daga kasar Gabon dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal itama daga kasar ta Ingila.