Labaran Wasanni
Ya kamata gwamnati tayi dokar gwada lafiyar ‘yan wasa – Dr. Ayodeji
Tsohon jami’in kula da lafiya na kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 17 ta kasa, Dr. Ayodeji Olarinoye, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya aiwatar da gwajin lafiya ga kowane dan wasa ya zama dole, kafin a fara gudanar da kowace gasa a fadin kasar nan.
Dr. Ayodeji Olarinoye ya bayyana haka ne yayin da yake maida martani kan mutuwar dan wasa Damilola yayin da ake tsaka da wasa a jihar Osun.
Damilola dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ofatedo dake jihar ta Osun, ya fadi ne sa’ilin da ake tsaka da gudanar da wasa a makon da ya gabata, inda ya kuma mutu kafin a garzaya asibiti dashi.
Dr. Olarinoye wanda ya kasance mai kula da lafiyar ‘yan wasan Golden Eaglets aji na shekarar 2013 da na 2015 da suka lashe kofin duniya na ‘yan kasa da shekara 17, ya ce, yanzu ne lokacin da ya kamata gwamnati a matakai daban-daban ta saka a matsayin doka yin gwajin lafiyar ‘yan wasa kafin gunarda da kowace a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login