Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta rubanya kokari wajen bunkasa ayyukanta- Sarkin Karaye
Mai martaba Sarkin Karaye Dr Ibrahim Abubakar na II, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta rubanya aikin da take yi na bunkasa jihar a fannoni daban- daban na cigaba a wa’adinta na biyu da zata yi.
Sarkin ya bayyana haka ne a yau a dakin taro na Africa House , dake fadar gwamnatin jihar Kano, inda ya jagoranci tawagar hakiman sa ziyara ta musamman ga gwamnan jihar Kano tare da taya shi murna.
Sarkin na Karaye Dr Ibrahim Abubakar na II, ya ce lokaci ya yi da shuwagabanni na mulki a dukkan matakai na Zamani da gargajiya zasu hada kai tare da yin aiki Kafada da Kafada ,tare da ajiye banbanci na siyasa, akidoji wajen yin aikin al’umma da bunkasa ta musamman ma wajen Ilimi, lafiya, tattalin arziki da harkokin tsaro.
Da yake jawabi gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin ta yanke shawarar kara darajar masarautun don samar da aiyyukan na musamman da suke a cikin birni wanda ba’a dasu a kauyuka wanda hakan zai bunkasa tare da rage cunkoson da ake samu na al’amura da dama a cikin babban birnin jiha.
Sarkin karaye ya rantsar da majalisar masarautar sa
Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano
Rikicin Gwamnatin Kano da masarauta: Dattawan Arewa za su yi Sulhu
A wani cigaban kuma, gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje , ya karbi sauran sarakuna uku na Gaya Ibrahim Abdulkadir , Rano Tafida Abubakar Ila, da na Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero, da suma suka ziyarci gwamnan a fadar gwamnatin jiha don taya shi murnar nasarar da ya samu wanda Kotun koli ta tabbatar da zaben sa a matsayin gwamnan jihar Kano.
Wakilin mu na fadar gwamnatin jihar Kano Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa, Sarakunan sun ziyarci gwamnan tare da dukkanin hakiman su, ya yin da gwamnan jiha da mataimakin sa Alhaji Nasiru Yusif Gawuna suka karbi bakuncin nasu.