Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ya kamata masu ruwa da tsaki su zuba jari a fannin bayar da horon da tsaro a Internet- Smartclicks

Published

on

Kungiyar nan mai zaman kanta, mai rajin bunƙasa harkokin Fasahar sadarwa ta Smartclicks Teach-Wellness, ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su bayar da fifiko wajen sanya hannun jari a fannin samar da tsafatatacciyar hanya da kariya ta  koyar da ilimin sana’oi ta kafar Internet

a fannin horas da matasa a harkokin da suka shafi fasahar Internet.

kungiyar, ta bukaci hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a wani bangare na bikin ranar tsafatatacciyar hanya da kariya ta kafar Intanet na shekarar 2025 wana ake gudanarwa a fadin duniya, an sadaukar da shi ne don wayar da kan jama’a game da samun kariya a kafar Internet. 

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabar kungiyrar ta Smartclicks Digital Life Skills Education, Suliyat Adeleye Idris ta bayyana cewa galibin iyaye da kungiyoyi na kashe makudan kudade wajen tabbatar da yara da kuma matasa sun samu kwarewa a fannin shiga duniyar Internet, sai dai ba kasafai aka fiya mayar da hankali ba wajen samar da tsaro da kuma tsaftace fannin.

Haka kuma,  ta kara da cewa, samun wadataccen ilimin da kwarewa a fannin kula da kuma tsaro a fannin na Internet zai kara taimaka wa matasa ba kawai su sami ƙwarewar a fannin ba, har ma da yadda za su samu kariya tare da rage irin tarin kalubalen da fannin ke fuskanta.

Sanarwar ta kuma ce, duk da cewa ana bikin ranar Intanet mai tsatsassuran tsaro sau daya a duk shekara, sai dai batun abu ne da ya kamata a rika dabbaka shi yau da kullum da kuma ya zama wajibi dukkan al’umma su sadaukar da kansu don samun aminci da zaman lafiya da ci gaban fasaha mai dorewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!