Kowane Gauta
Ya kamata mutane su fahimci manufar shugaba Buhari – Barista Ismail Ahmad
Barrista Ismail Ahmad yace bai kamata mutane su rika kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba saboda irin manyan ayyukan raya kasa da gwamnatin ke yi domin ciyar da kasar gaba.
Ismail Ahmad ya bayyana haka ne ta cikin shirin Kowane Gauta na gidan Radio Freedom Kano.
Batista Ismail ya kara da cewa kamata ya yi mutane su sani cewa karin kudin mai da kuma na wutar lantarki da aka yi a yanzu an yi ne badan a muzgunawa talakawan kasa ba an yi da nufin ciyar da kasar nan gaba.
Ya kara cewa kowa yasan talawan Najeriya ne kadai ke goyan bayan gwamnatin shugaba Buhari musamman wajen ayyulan data dakko na ciyarda Najeriya gaba.
You must be logged in to post a comment Login