Kasuwanci
Ya zama wajibi a biya Kamfanonin da ke kan tsarin Band “A” diyya- NERC

Hukumar da ke kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya NERC, ta ce, ya zama wajibi kamfanonin rarraba wutar lantarki su biya diyya ga kwastomomin da ke rukunin ‘Band A’ bisa rashin ba su wutar da ta gaza ta sa’o’i 20 kamar yadda yake a doka.
Daga Cikin wadanda za a biya diyyar har da babban bankin kasa CBN, da ofishin jakadancin China a kasar da kuma wasu mutanen da ke unguwanni 557 a fadin Najeriya.
Tuni dai wadanda abun ya shafa suka fara yaba wa da daukar wannan mataki da ake ganin cewa idan zai ci gaba za a samu raguwar matsalolin da suka dabaibaye fannin rarraba wutar lantarki.
You must be logged in to post a comment Login