Manyan Labarai
Ya zama wajibi shugaba Buhari ya kawo karshen cin zarafin Musulmi- Kungiya
Gidauniyar mata Musulmi ta Kano ,ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran jami’an tsaron kasar nan suyi gaggawar kawo karshen cin zarafin ‘yan uwa Musulmai a yankin Arewacin kasar nan ,musammman satar yaran musulmi da sauya musu addini zuwa kiristoci.
Sakatariyar Gidauniyar Hajiya Fatima Ibrahim Ilyasu Dorayi ce tayi kiran a wani taron manema labarai da gidauniyar ta gudanar kan cin zarafin da ake yiwa Musulmai a Arewacin Najeria.
Hajiya Fatima ta yi Allah wadarai kan yadda aka gano wani Kirista mai suna Solomon ya sato ‘yan gudun hijira na Boko Haram sama da dubu hudu da boye su a gidan sa, yana azabtar dasu tare da yiwa mata fyade wanda tace hakan tamkar tozarta Musulunci ne.
Sakatariyar Gidauniyar Fatima Dorayi ta kara da cewa irin wadannan abubuwa da ake yiwa Musulmi musamman a Arewaci da sauran gurare na tozartawa kamata yayi , ya zama darasi akan Musulmi wajen komawa ga Allah domin samun makoma mai kyau.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito Gidauniyar na kira ga Gwamnan Kano da Masarautar Kano da sauran mahukunta suyi kokarin daukar matakin shari’a kan duk masu kokarin tayar da zaune tsaye a Najeriya.