Rahotonni
Yadda aka yi bikin ranar fadakarwa kan illar kashe kai ta duniya
Daga Hafsat Danladi Abdullahi
Hukumar lafiya ta duniya WHO tare da hadin gwiwar kungiya mai rajin kare kai daga illar kashe kai ta duniya ta kebe duk ranar 10 ga watan Stumba kowacce shekara ta zamo ranar fadakarwa dangane illar kashe kai ta duniya
Kungiyoyin biyu sun ware ranar da nufin zakulo hanyoyi da za’abi dan gano hanyoyin da zabi wajen hana matasa aikata kashe kai.
A binciken da hukumar lafiya ta duniya da WHO da kungiyoin suka gudar sun bayyana cewa matsalolin da suke hadasa kashe kai sun hada da talauci, da kyama ko kuma wata damuwa dake damun masu aikata wannan mumunan dabi’a.
An dai fara bikin rana rana fadakarwa dangane illar kashe kai ta duniya a shera 2014 domin a wayar da kan mutane da su guji aikata dabi’ar ta kashe kai
Freedom ta tattauna da wasu mutane kan me jawo ake aikata dabi’ar ta kashe kai?
“Sun bayyana cewa abunda kesa mutane suke kashe Kansu shine damuwa da rashin ilimi da kuma talauci”
A nasa bangaren masani halayar dan Adam DR Maikano Madaki na sashin halayyar dana dam na jami’ar Bayero dake nan Kano yace dalilin da yake sa mutane ke aikata dabi’ar bai wuce ciwon damuwa ba wato depression
“Yace ciwon damuwa ne yake jawo su kashe Kansu idan kwakwalwa ta jirkita sai ta baka cewa ka kashe kanka”.
Ya kuma ce abunda ke jawo yawaitar da Kashe kai shine yawan shan miyagun kwayoyi
“Yace abunda ke hadaswa shine shan miyagun kwayoyi da kuma sa damuwa kana da tsadar rayuwa”.
Masani yace hanyoyin daza abi wajen magane yawaita kashe kai shine mutane su rage sa damuwa a ran su ko kwallafa wani abu da bai taka-kara-ya-karya-baya.
DR Mai kano Madaki ya yi kira ga mutane da suyi amfani da rayuwa su ta hanyar da ta dace
Taken bikin na bana shine “wayar da kan mutane kan illar kasha kai da wasu mutane ke yi kan damuwa”
You must be logged in to post a comment Login