Labarai
Yadda aka yi bikin ranar wanzar da zaman lafiya ta duniya a Kano
Masanin halayyar dan Adam dake jami’ar Bayero a nan Kano, ya bayyana rashin zaman lafiya da cewa daya ne daga cikin Abubuwan da ke hana tattalin arzikin kasa bunkasa.
Dakta Maikano Madaki shi ne ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakiliyarmu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar kauracewa tashe-tashen hankula ta duniya da ake gudanarwa a yau.
Ya ce, ranar na mayar da hankali wajen tunawa da wadanda Suka yi yaki kan kauracewa tashin hankali a dadin duniya tare da fito da sabbin dabaru na tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Majalisar Dunkin duniya ce dai ta ware duk ranar biyu ga watan oktobar kowacce shekara don karrama shugaban kasar India Mahat Maghandi Wanda ya jagoranci samun yancin Kai da zaman lafiya a kasar ta India.
Muna dauke da cikakken rahoton bikin ranar a labaran mu na gaba.
You must be logged in to post a comment Login