Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Buhari ya dauki matakin rufe layukan wayoyin da ba’a yiwa rijista ba

Published

on

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa daga ranar 30 ga watan da muke ciki na disamba za a rufe dukkan layukan wayoyin salular da ba’a yiwa rajista ba.

Wannan dai na daga cikin shawarwarin da aka cimma a wani taron gaggawa da ma’aiktar sadarwa ta kasa ta kira a Abuja.

Mai magana da yawun hukumar sadarwa ta kasa , Ikechukwu Adinde ya ce an kira taron ne sakamakon umarnin dakatar da yiwa sabbin layukan wayoyi rajista da kamfanonin sadarwa suka yi.

Ya ce an kafa wani kwamatin karta kwana da ya hada ministoci da sauran masu fada aji domin rufe dukkan layukan wayoyin da basu da rajistar a karshen watan na disamba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!