Labarai
Yadda Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar zartar ta kasa ta kafar Internet karo na 14, a babban birnin tarayya Abuja.
An dai fara taron ne da misalin karfe 10 na safe bayan da aka kammala taken Najeriya.
Daga cikin wadanda suka halacci taron akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin Boss Mustapha.
Sauran su hada da ministoci guda 8 ya yin da kuma aka hange shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Dr, Folasade Yemi-Esan.
Daga cikin ministocin akwai Rotimi Amaechi miistan Sufurin jiragen kasa da sanata Hadi Sirika ministan sufurin jiragen sama da Dr, Osagie Ehanire
Daga ciki akwai ministan lafiya da Zainab Ahmed da Abubakar ministar Kudi da Abubakar Malami ministan shari’a da Babatunde Fashola ministan lantarki da Lai Mohammed ministan yada labaai da kuma DR, Isa Ali Pantami ministan sadarwa na zamani
You must be logged in to post a comment Login