Labarai
Yadda Buhari ya sanya hannu akan kasafin kudin badi
Da misalin karfe 12 da minti 45 na ranar yau Alhamis ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kasafin kudin badi.
Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin badin ne a fadar sa dake babban birnin tarayya Abuja, kwanaki biyar bayan da majalisar dokoki ta kasa ta kammala taza da tsifa na kasafin kudin badin.
A dai ranar 21 ga watan Disamba mai karewa majalisar dokokin ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirin kasafin kudin wanda za’a kashe fiye da Naira tiriliyan 13.
Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen sadarwar zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafin sa na Twitter.
Sanya hannu akan kasafin kudin na nuna cewar, ya zama doka, wanda kuma kae hasashen cewar za’a aiwatar da wasu manyan ayyuka a cikin kasafin kudin.
Muna dauke da cikakken labarin a nan gaba kadan
You must be logged in to post a comment Login