Addini
Yadda farashin kayayyakin abinci ya ke a birnin Kano a ranar 16 Ramadan – Muhyi Magaji
Ga farashin kayayyakin abinci wanda hukumar karbar korafe-korafe da yaki da hanci da rasahawa ta jihar Kano karkashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ta dauke nauyi domin tabbatar da cewa ‘yan kasuwa basu boye ko sun karawa kayan kudi ba.
Babban Buhun shinkafa ya fara ne daga Naira dubu goma sha tara zuwa dubu ashirin da biyu da dari uku.
Karamin buhu kuwa ana sayar da shi dubu goma zuwa dubu goma sha daya da ɗari biyar.
Buhun sukari kuwa Naira dubu goma sha takwas da dari takwas, kwano kuma Naira dubu daya da dari da hamsin.
Buhun Fulawa kuwa ana sayar da shi Naira 13,800 zuwa 14,200. Kwano daya ko koma 650.
Farashin jirkar farin mai ya fara daga dubu Naira 19 zuwa 19,000.
Sai Lita 10 da ake saidawa Naira dubu 7,300, 8,500 zuwa dubu 9,300.
Buhun Wake kuwa yana kamawa daga Naira dubu 39,000 zuwa 40500 yayin da ake aunar da kwano daya akan 1,050.
Gero Buhun dubu 21k. Kwano kuma kwano 550.
Ana saida Taliya 4,200 zuwa dubu 4,850.
Makaroni 3,900 zuwa 4,200.
Yadda farashin kayan abinci ya kasance kenan a wasu daga kasuwanni Kano wanda hukumar karbar korafi da yaki da hanci da rasahawa ta jihar Kano karkashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ta dauke nauyi domin tabbatar da cewar ‘yan kasuwa basu boye ko sun karawa kayan kudi ba.
You must be logged in to post a comment Login