Connect with us

Labaran Kano

‘Yan sanda sun kara ceto yara biyu da aka sace a Anambra

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta cafke wasu mata 3 da aka samu da kananan yara guda biyu ‘yan kimanin shekaru 2 zuwa 4, an cafke matan ne a yankin kasuwar Nkpor/Tarzan Junction dake karamar hukumar Idemili ta arewa dake jihar Anambra.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra SP. Haruna Muhammad ta bayyana cewa izuwa yanzu dai basu kai ga gano asalin inda iyayen yaran suke ba, amma dai suna cigaba da bincike.

Shima a nasa bangaren kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana Freedom Radio cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta aiko musu da wannan bayani kuma suna kira ga al’umma ga duk wanda ya san wadannan yara to ya hanzarta ya tuntubesu.

Duba hotunan yaran a kasa:

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Yadda hukumar Hisbah ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwarta

Yaran Kano 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike na musamman

Ina yabawa ‘yan sandan jihar Kano –Magajin garin Daura

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,500 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!