Labarai
Yadda jami’an tsaro suka kama Maina a Jamhuriyyar Niger
Jami’an hukumar leƙen asiri da haɗin gwiwar wasu jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar nan sun cafke Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin lura da fanshon ma’aikata, a wani gari da ke jamhuriyar Nijar da yammacin jiya Litinin.
Jaridar Intanet ta Daily Nigerian ta rawaito cewa wani babban jami’in leƙen asiri da ba a bayyana sunansa ba, ya shaida cewa an samu nasarar kama Mainan ne saboda alaƙar da ke akwai da kuma yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen biyu da je maƙwabtaka da juna.
A makon jiya ne dai wata babbar kotun tarayya ta kama Sanata Ali Ndume bisa rashin Maina, kasancewar shi ne ya tsaya masa a kotun har ta bayar da belinsa.
You must be logged in to post a comment Login