Labarai
Yadda ma’aikata za su bibiyi hakkin su-hukumar kyautatuwar ma’aikata
Babbar sakatariyar dake kula da hukumar kyautatuwar ma’aikata ta jihar kano, Hajiya Binta Fatima Salihu ta ce, babban kalubalen da suke fuskanta shi ne al’umma ba sa zuwa kai korafi a duk lokacin da suka ci karo da wanda ya tauye musu hakkinsu.
Hajiya Binta Fatima Salihu ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin ‘‘Barka da Hantsi’’ na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan yadda ma’aikatan gwamnati za su rika neman hakkokinsu idan an tauye musu.
A cewar Fatima Salihu kowanne Ma’aikaci na da damar kai korafin cewa an tauye masa hakki ko kuma zargin cin zarafinsa
Haka kuma ta bayyana cewa akwai hukuncin da suke dauka kan dukkan ma’aikacin gwamnati da aka kama yana musguna wa al’umma da kuma yin wasarere da aikinsa.
Babbar sakatariyar a hukumar Kyautatuwar ma’aikata ta kuma yi kira ga dukkan sauran kungiyoyin da ke fafutukar taimakawa hukumar da su cigaba da bata gudunmawar ta hanyar da ta dace.