Labarai
Yadda majalisar dokoki ta Jigawa ta yi wa dokar wa’adin shugabannin kananan hukumomi garanbawul
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta mayar da wa’adin shugabannin kananan hukumomi zuwa shekaru uku-uku zango biyu maimakon shekaru bibiyu.
Wannan ya biyo bayan gyaran fuska ga sashe na 6 (1) na dokar kananan hukumomi ta 2012 ya yin da duk wanda ya shugabanci kananan hukumomi a zango shekaru biyu a jere ba zai sake tsayawa zaben wannan mukami ba.
Haka kuma gyaran fuskar ya shafi sashe na 9 (1) wadda ya baiwa gwamna ikon dakatarwa ko kuma sauke duk wani shugaba ko mataimakin shugaba ko kamsila zababbe ko nadadde da aka samu da aikata ba dai-dai ba bayan samun amincewar majalisar.
Gyaran fuska ga karamin sashe na biyu na sashe na 9 kuwa ya baiwa majalisar dokoki ikon saukewa ko dakatar da shugaba ko mataimakinsa ko kamsila maras gafaka da mai gafaka daga kan mulki bayan kotu ko kwamatin majalisar ya same shi da aikata ba dai-dai ba.
Sai kuma sashe na 67 (6) (A) da ya ayyana sakatare da Daraktan mulki da ma’aji a matsayin masu ikon rattaba hannu kan takardun kashe kudaden kananan hukumomi.
A wani labarin kuma, majalisar dokokin jihar Jigawa ta sahalewa kwalejin ilimi dake Gumel ta sake dawo da ayyukan cibiyoyinta na koyar da karatun shedar malanta ta NCE bisa tsarin karatu daga gida wato distance learning a fadin jihar nan.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in yada labarai ta kafar Internet Saf’one Sani Imam ya sanya wa hannu cewa, matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamatin ilimi wadda ya bayyana cewa ciyoyin na rufe wadda hakan zai kawo nakasu ga malamai da ba su da shedar malanta ta kasa.
You must be logged in to post a comment Login