Labarai
Yadda masarautar Kano ta dakatar da mai Unguwa kan saida jariri
Majalisar masarautar Kano ta dakatar da mai unguwar Sabon gari dake karamar hukumar Fagge Alhaji Ya’u Mohammad saboda zargin yana da hannu wajen saida wani yaro dan shekara daya.
Mai unuwar ta sabon gari wanda ya ake zargin da saida yaron ta hannu kwamandan Hisbah na karamar hukumar Hisbah ta Fagge Jamilu Yusuf.
Wannan na kunshi cikin sanarwar da sakataren galadiman Kano Abbas Sunusi, Muhammad Umar ya fitar a madadin majalisar masarautar Kano cewa an dakatar da dagajin Alhaji Ya’U Mohammad kan zargin wannan badakalar a jiya Talata.
Muhammad Umar ya ce majalisar masarautar Kano ta yanke shawarar dakatar da mai unguwar ne har sai hukumar hana safara da fataucin bil adama ta kasa NAPTIP ta kammala bincike.
Hukumar NAPTIP na binciken dagacin karamar hukumar Fagge Alhaji Yau Mohammad tare da kwamandan Hisbah na Faggen Jamilu Yusuf kan zargin saida jariri ga wata mace kan Naira dubu 20.
You must be logged in to post a comment Login