Labarai
Yadda masu Ƙananan Masana’antu na Dakata suka yi wa KEDCO Alƙunutu
Masu kanana da matsakaitan masana’antu a yankin Dakata da ke nan Kano, sun gudanar da Sallar Alkunutu ga KEDCO.
Wadanda suka yi wannan Sallah dai, sun zargi Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano KEDCO da hana su wutar da suke yin amfani wajen gudanar da masana’antun.
Mutanen sun gudanar da Sallar ne da safiyar yau Laraba a rukunin masana’antun na Dakata.
Da ya ke jawabi kan maƙasudin Alkunutun, shugaban ƙungiyar masu masana’antu yankin Malam Surajo Musa, ya ce, yanzu haka sun shafe kusan watanni uku ba sa samun wutar da suke amfani da ita.
You must be logged in to post a comment Login