Manyan Labarai
Yadda tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ya kalubalaci Buhari
Tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Mike Ejiofor, ya kalubalanci shugaba Buhari da ya tabbatar ya samar da sauyi da kuma ci gaba a shekara mai kamawa ta 2021 ta hanyar sauke dukkanin hafsoshin tsaron kasar tare da maye gurbinsu da sabbi don kyautata tsaro.
Tsohon shugaban na bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka da shi a gidan talabijin na Channels.
Ya ce, Najeriya na bukatar sauyi da ci gaba musamman na yaki da ayyukan ta’addanci da masu garkuwa da mutane da ‘yan boko haram da sauran manyan laifuka.
Mike, ya kara da cewa akwai bukatar shugaba Buhari ya sauya ta bangaren samar da kayan aiki da kuma sauke mataimakansa na bangaren tsaro musamman hafsoshin tsaron kasar.
A don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki a Najeriya da suka hadar da majalisaun wakilai dana dattijai da su tabbatar da sun bada goyon baya wajen sauke hafsoshin tsaron kasar tare da samar da sabbi don kyautata tsaro a kasar.
You must be logged in to post a comment Login