Manyan Labarai
Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana
Daga gasar cin kofin Zakarun nahiyar turai wato Champions league, wasannin da suka gudana a yau , kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea ta Debi kashin ta a hannu bayan da ta sha jibga a hannun kungiyar Kwallon kafa ta Bayern Munich dake kasar Jamus (Germany ) a wasan farkon zagaye na biyu na gasar .
Tun da fari, bayan dawowa sa ga hutun rabin lokaci dan wasan Bayern Munich Serge Gnabry, ne ya zura Kwallo a ragar Chelsea a minti na 51, bayan samun taimako daga hannun dan wasa Robert Lewondowski, ya kuma sake zura Kwallo ta biyu , a minti na 54, shima biyo bayan wani taimakon da ga wajen Lewondowski din karo na biyu.
Ya yin da Lewondowski ya zura Kwallo ta uku a minti na 76, ta bangaren taimakon Alphonso Davies, inda Alkalin wasa Clement Turpin dan kasar Faransa ya kori dan wasa Marcos Alonso ,na kungiyar Chelsea da Jan kati a minti na 83 ana dab da a tashi daga wasan, sakamakon ketar da ya kaiwa dan wasa Lewondowski.
Gwamnatin Kano za ta kashe sama da miliyan 98 a bangaren wasanni
Rahoto : Nazari kan wasanni na gida tana ketare
Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana
A wasan Napoli da Barcelona, an tashi wasa kunnen doki wato 1 da 1, a minti 30 din farkon rabin lokaci dan wasan Napoli Dries Marten , dan kasar Belgium ya zura wa kungiyar ta sa Kwallo bayan samun taimakon daga hannun Piotor Zielinski, wanda Jim kadan bayan dawowa hutun rabin lokaci a minti na 57, Antoine Griezmann, na kungiyar Barcelona ya rama mata Kwallon ta, bayan samun taimakon bugun kwibi daga hannun dan wasa Nelson Samedo.
Alkalin wasa Felix Brych dan kasar Jamus (Germany ), ya kori dan wasan Barcelona Arturo Vidal, da katin kora na Ja bayan samun katin gargadi na Rawaya wato Yellow a Jere har guda biyu, A minti na 89 na wasan, sai yan wasa Lionel Messi, Sergio Busquest, da Griezmann, da duka suka samu katin gargadi na dorawa.
Za dai a fafata wasa na biyu, na zagayen a ranar Larabar 18 ga watan Maris mai kamawa , a biranen Munich da Barcelona.
Rahoto: Daga Aminu Halilu Tudun wada
You must be logged in to post a comment Login