Labarai
Yadda ‘Yansandan Kano suka cafke wadanda suka kone magidanci

Yadda ‘Yansandan Kano suka cafke wadanda suka kone magidanci
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta Sami nasarar cafke mutanen da suka kona magidanci da ‘yar sa Mai shekara 2 da mai dakin sa Mai tsohon ciki.
A daren ranar Talata da ta gabata ne aka wayi gari wasu sun bi dare sun garkame wannan magidanci a gidansa suka kuma cinnawa gidan wuta yayi sanadiyar rasuwar sa, da mai dakinsa kuma mai tsohon ciki da kuma ‘yar karamar yarinya.
Rundunar ta kama wanda ya jagoranci wannan aika-aika ne lokacin da yayi yunkurin yin basaja don ficewa daga nan jihar Kano.
muna dauke da cikakken labarin a nan gaba.