Labaran Kano
Yadda zaman majalisar dokokin Kano ya kasance a yau
Majalisar dokoki ta jihar Kano, ta kafa Kwamitin wucin gadi na mutane 7 da zai zagaya yankunan da ake fama da ƙamfar ruwa tare da gudanar da bincike kan matsalar.
Kafa Kwamitin dai ya biyo bayan kudirin hadin gwiwa da dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gaya Alhaji Abubakar Dabladi Isa ya gabatar a madadin shi kansa da wakilan ƙananan hukumomin Wudil da Warawa da kuma ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
Kudirin dai ya bukaci gwamnatin jiha kan ta sake tona rijiyoyin samar da ruwa a matatar ruwa ta Wudil tare da sanya sabbin kayan aiki domin samun wadataccen ruwan famfo a yankunan nasu.
Majalisar ta kafa Kwamitin ne karkashin jagoracin mataimakin mai tsawatarwa na majalisar Hayatu Musa Ɗorawar Sallau, tare da bada mako guda domin Kwamitin ya gabatar da rahotosa
Haka dai a zaman majalisar na yau Talata, Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwale a zauren majalisar Yusuf Babangida Sulaiman ya gabatar da kudiri na bukatar gwamnatin jihar Kano ta gaggauta kammala ayyukan gina magudanan ruwa da gwamnatin ta bada kwangilar yi amma aka yi watsi da ayyukan bayan da aka fara.
Da yake gabatar da ƙudurin Yusuf Babangida Sulaiman ya ce, an dade da fara aikin a unguwannin Sabon Sara da Hausawa Lokon Liman da kuma Diso sai dai tun ba a ci Talata da Laraba ba Ɗan kwangilar ya tattara kayansa aikin ya tsaya inda yara ke fadawa cikin ramin lambatu din sannan rodikan da aka zuba ba tare da an rufe su ba ke fasa tayoyin ababen hawa.
Wakilinmu na majalisar dokokin Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa Ɗan majalisar mai wakiltar Gwale ya bukaci gwamnati ta sanya a kammala aikin ba da jimawa ba la, akari da cewa yanzu haka ana tsakiyar damina.
You must be logged in to post a comment Login