Kiwon Lafiya
Yajin aiki: karo na biyu an sanya hannu kan yarjejeniyar janye yajin aikin likitoci masu neman kwarewa da gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta sake sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tare da kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa kan batun janye yajin aikin da suke yi.
Wannan dai shi ne karo na biyu, da gwamnatin tarae da kungiyar likitoci masu nem,an kwarewar ke sanya hannu kan yarjejeniyar cikin makwanni biyu.
Tun da fari dai an sanya hannu kan yarjejeniyar ta farko a ranar 31 ga Maris amma daga baya likitocin da ke yajin suka ki amincewa.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya bayyana hakan a Asabar din nan, jim kadan bayan rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsakanin tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da na NARD.
Ngige ya ce taron karo na biyu ya zama dole, domin kuwa shi zai bada damar gyara yarjejeniyar ta farko, domin kuwa akwai kura-kurai wajen biyan albashin ma’aikatan, yayin da wasu basa samun albashin su.
“Dangane da wannan halin, an kafa kwamiti na mutum biyar don bayyana jerin sunayen jami’an da abin ya shafa kuma mun basu awanni 72 don su mika takardar sunayen” in ji Cris Ngige.
You must be logged in to post a comment Login