Labarai
Yaki da ta’adda: an cafke ‘yan fashi 9 a jihar Bauchi
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wasu ‘yan fashi 19 a ranar 18 ga watan Nuwamba a kauyen Gudum Hausawa.
Gungun ‘yan fashi da makami sun shiga kauyen Gudum Hausawa ne a wani hari da suka kai yankin, sai dai tuni babban jami’in ‘yan sanda na yankin ya jagoranci tawagarsa tare da kamo su.
Cikin wadanda aka kama din sun hadar da:
Ahmed Umar mai shekara 22 da Mohammed Danladi dan shekara 20 sai kuma Abdulsalam Ali mai shekara 22 da kuma Abdulmumni Zakari Ya’u dan shekara 18.
Sauran sune: Umar Aliyu dan shekara 21 da Ibrahim Ahmed mai shekara 21 sai Ahmed Adamu mai shekara 18 sai kuma Usman Yunusa dan shekara 18 da kuma Basiru Sabo mai shekara 18.
A yayin da ake bincikensu, an same su da rafar kudi guda 9 da yadin shadda 5 da na’urar kwamfuta Laptops 3 da kuma dutsen guga 1 sai wayoyin hannu 3 da baburin Roba-roba 2 da kuma kimanin naira dubu casa’in.
A bangaren makamai kuwa, an same su da adda guda 7 da wuka 1 da gwalagalwai “yari da zobe” da kuma takalmi mai tsada guda 1.
You must be logged in to post a comment Login