Labarai
Yan bindiga sun kai hari kan jerin gwanon motocin tsohon ministan sufuri

Wasu yan bindiga sun kai hari kan jerin gwanon motocin tsohon ministan sufurin kasar nan Rotimi Amaechi
Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ranar Juma’a a kan titin Ubima zuwa Omuanwa da ke ƙaramar hukumar Ikwerre a jihar Rivers
A lokacin da lamarin ya faru, tsohon gwamnan na jihar Rivers yana kan hanyarsa ta zuwa garinsu Ubima domin yin rajista a hukumance a matsayin mamba na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a mazabarsa.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi ƙoƙarin yi wa ayarin motocin nasa kwanton bauna, amma jami’an tsaro da ke rakiyar tsohon ministan sun yi nasarar fatattakar su.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu rahoton jikkata ko mutuwa sakamakon harin ba
You must be logged in to post a comment Login