Connect with us

Labarai

Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke yankin Bukuyum

Published

on

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda suka halaka mutum ɗaya tare da sace mutane biyar, a daren ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen tun cikin dare har zuwa wayewar gari.

Wani mazaunin ƙauyen, Malam Sani, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen da dare, inda suka halaka mutum ɗaya, suka sace mutane, sannan suka harbe wani mutum da ya samu mummunan rauni, wanda aka kai shi Asibitin koyarwa na Sokoto domin jinya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro suna kokari domin kubutar da wadanda aka sace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!