Labarai
‘Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Dafur
A karon farko cikin shekaru da dama ‘yan bindiga sun kashe mutune 20, ciki har da yara kanana a yankin Dafur na kasar Sudan da yaki ya dai-dai-ta.
Wani shugaban ‘kabila ya bayyana cewa wannan na zuwa ne biyo bayan cimma wata yarjejeniya da masu gonaki cewar za su koma bakin aikin su na noma, sai dai a yammacin jiya ne ‘yan tada kayar baya suka bude musu wuta tare da kashe mutane 20 ciki har da mata da kananan yara.
Lamarin ya faru ne a yankin Aboudous dake nisan kilomita 90 daga kudancin Nyala, babban birnin kudancin lardin Darfur.
A shekarar 2003 ne rikici ya barke a yankin Dafur tsakanin kabilu ‘yan tsiraru da ‘yan tawaye masu biyayya ga tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir.
Majalisar dinkin duniya ta ce rikicin na yankin yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 30, kana kuma ya raba miliyan 2 da rabi da muhallansu.
A cikin watan Afrilun shekarar 2019 ne aka hambarar da gwamnatin shugaba Omar Al-Bashir, biyo bayan watanni da aka kwashe ana zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.
You must be logged in to post a comment Login