Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan jarida na da muhimmiyar gudummuwa wajen wanzar da zaman lafiya – Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa Dan jarida yana da muhimmiyar rawa da zai taka wajen wanzar da zaman lafiya da ciyar da kasa gaba tare da samarwa al’umma walwala.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kano karkashin shugabanta Kwamared Abbas Ibrahim yau a fadarsa.
A nasa bangaren shugaban kungiyar ta NUJ Kwamared Abbas Ibrahim ya sha alwashin yin duk me yiwuwa don ganin ‘yan jarida a jihar Kano suna gudanar da aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.
Wakilinmu na fadar Sarkin Kano Muhammadu Harisu Kofar Nassarawa ya ruwaito cewa, makarantar Islamiyar ta marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da ke Gwangwazo ta kai ziyarar ban girma zuwa fadar Sarkin karkashin jagorancin shugaban makarantar, Alhaji Muhammad Sidi Ali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!