Coronavirus
‘Yan kasuwa sun nemi Ganduje ya bude Kasuwanni sau biyu a mako
‘Yan Kasuwa sun bukaci gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ya duba dokar kulle na zaman gida tare da bada dama ga ‘yan Kasuwannin Sabongari da Kwari da na Singer domin fitowa Kasuwancin su a kebabbun ranakun da aka ware a mako don gudanar da nasu Kasuwancin.
Alhaji Imamu Tafida, Tafidan Dakayyawa kuma daya daga cikin Dattijan Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, wato Sabongari shi ne yayi wannan kira duba da mawuyacin halin da ‘yan Kasuwan suke ciki kamar yadda jagororin Kasuwar suka tabbatar.
Alhaji Imamu Tafida, ya ce ‘yan kasuwa da dama, sun tafka asara ta miliyoyin nairori sakamakon rufe kasuwannin, kasancewar kayan da suka siyo basu shigo ba dalilin hana shige da fice, hakazalika wanda ake dasu a kasuwar ba a siyar dasu ba.
Tafidan Dakayyawan, ya kuma bada tabbaci ga gwamnati na cewar zasu yi duk mai yiwuwa wajen daukar matakan kariya daga cutar ta Corona daga bangaren su da masu mu’amala dasu da zarar an basu damar gudanar da Kasuwancin su.
Wakilin mu, Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa, Alhaji Imamu Tafida, ya bukaci al’umma dasu bi umarnin hukumomi da ma’aikatan lafiya, tare da rubanya addu’a domin ganin an kawar da wannan annoba da ta kawo tsaiko a al’amuran yau da kullum na jama’a.
You must be logged in to post a comment Login