Labarai
Yan Kasuwar Badawa sun nemi daukin gwamna bayan rusau din KNUPDA

Wasu masu gudanar da sana’o’i a unguwar Badawa yankin Agangara da ke Karamar Hukumar Nassarawa a Kano, sun nemi daukin gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Injinya Abba Kabir Yusuf don neman ta mayar musu da filayen su da da gwamnatin baya ta gwamna Ganduje ta rushe musu shaguna.
A zantawarsu da Freedom Radio, mutanen sun bayyana cewa sun mallaki wurin ne tun shekaru da dama da suka gabata, sai dai, hukumar Tsara birane ta KNUPDA karkashin gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta rushe musu shagunan ba tare da sanar da su ko basu wa’adin barin wurin ba, kuma ba a biya su diyya ba.
Mutanen wadanda suka hadar da maza da mata, sun ce, sun mallaki filin wurin ne tun a shekarar 1985, inda suka gina tare da fara gudanar da kasuwancinsu, sai dai sun shiga halin kunci tun bayan rushe musu shagunan.
Haka kuma ‘yan kasuwar, sun koka tare da yin zargin Mai unguwar yankin Malam Umar Kasim Adamu, inda suka ce, shi ma da kansa ya na jagorantar yaransa inda suke zuwa suna rushe musu shagunan.
A nasa bangaren, a zantawarsa da Freedom Radio ta wayar tarho, Mai unguwar Yankin Malam Umar Kasim Adamu, ya musanta cewa ya na da hannu a yin rusau din inda ya bayyana cewa aikin hukumar tsara birane KNUPDA.
Haka kuma Mai unguwar, ya ce, hukumar KNUPDA da tallafin Hisbah ne suka gudanar da aikin rusau din bayan da mutanen suka ki bin umarnin da gwamnati ta basu na daina sayar da Barasa da Naman Kare da kuma wasu sauran nau’ikan kaya maye.
Sai dai ko da wakilinmu Auwal Hassan Fagge, ya tuntubi mai magana da yawun hukumar ta KNUPDA Hajiya Bahijja Malam Kabara, wadda ba ta bari an nadi muryarta ba, ta bayyana cewa suna kan bincika wa don tabbatar da abinda ya faru kasancewa tun a gwamnatin baya aka rushe wajen.
You must be logged in to post a comment Login