Kasuwanci
Yan kasuwar Kano na fargabar daina karbar tsofaffin kudi
Yan kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano, sun koka kan yadda harkokin cinikinsu ya ja baya.
Yan kasuwar, sun alakanta hakan da kusantowar wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi da babban bakin Najeriya CBN ya sanya.
Haka kuma sun bukaci da a kara wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudin na Naira 200 da 500 da kuma 1000.
Yanzu haka dai, wasu yan kasuwar sun fara sanar da abokan huldar su cewa za su daina karɓar tsofaffin kuɗin daga yau Asabar, yayin da wasu kuma suka ambata ranar Litinin da kuma Talatar makon gobe.
Haka kuma wasu cikin yan kasuwar cewa suka yi daga ranar Laraba sai dai mutum ya tura musu kudin kayan da ya saya ta asusun su kai tsaye watau Transfer ko kuma ya ba su sabon kuɗi.
Sakataren wata kungiya da ke kula da harkokin baki ‘yan kasar waje a kasuwar ta kantin kwarin Musa Umar Sanda Arzai, ya shaidawa Freedom Radio cewa ‘A kungiyance ba mu fitar da sanarwar daina karbar tsohon kudi ba’.
Ya kuma ce, “Daina karbar kudaden a yanzu zai jefa kasa cikin matsin tattalin arziki sakamako sababbin basu yawaita a hannu jama’a”.
Musa Umar Sanda, ya kara da cewa “Ya kamata CBN ya kara yin nazari kafin ya dena karbar kudaden a karshen watan nan na Janairu”.
You must be logged in to post a comment Login