Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan Nigeria na ci gaba da korafi kan sababbin takardun kudi

Published

on

Central Bank Of Nigeria
  • Karancin saababbin kudi ya jefa yan Najeriya cikin shakku
  • har yanzu yan Najeriya da dama ba su ga sabon kudin kasar ba
  • Al’umma sun bukaci CBN ya tsawaita lokacin karbar tsofaffin kudi

Yayin da ya rage kasa da makonni biyu a daina karbar tsofaffin kudin Najeriya, mutanen da dama sun bayyana damuwarsu bisa karancin takardun sabbin kudin.

Yanzu haka dai, an kwashe kwanaki goma sha bakwai da fitar da sabbin takardun kudin da suka hada da Naira 200 da 500 da kuma 1, 000.

Sai dai tun bayan da babban bankin kasa CBN ya fitar da sababbin kudin, mafi yawa daga cikin yan Najeriya suna cewa har yanzu ba su taba ganin sabon kudin ba.

Rubutu masu alaka: https://freedomradionig.com/mun-fara-raba-sabbin-kudin-naira-a-bankuna-cbn/

BBC ta ruwaito cewa, yan Najeriya da dama sun nuna damuwa bisa yadda sabon kudin ke wahalar samu a bankuna da injinan cirar kudi watau ATM.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!