Labarai
‘Yan majalisa sun yi Allah wadai da karuwar matsalar tsaro a Najeriya
Majalisar wakilai da ta dattijan kasar nan, sun yi Allah wadai bisa yadda ake samun karuwar matsalar tsaro a kasar.
Majalisun biyu sun bayyana takaicinsu kan yadda aka sace sama da dalibai dari uku a makarantar kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina a baya-bayan nan.
Kazalika majalisaun biyu sun ce babu bukatar gayyatar ministan tsaro da sauran hafsoshin tsaron kasar da na hukumar sirri ta DSS kan batun tattauna sace daliban a makon da ya gabata.
A don haka suke bukatar shugaba Buhari da ya gagguta samar da mafita ga me da sha’anin tsaro a Najeriya, musamman a fannin garkuwa da mutane da kuma kashe su.
Shugaban majilsar dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ce za su ci gaba da hada kai da dukkanin shugabanni don tabbatar da an kawo karshen matsalar tsaro da ya addabi kasar.
You must be logged in to post a comment Login