Kiwon Lafiya
‘yan Najeriya basu amfana da mulkin dimukuradiyya baFarfesa-Jega
Tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya INEC Farfesa Attahiru Jega, ya ce mulkin dimukuradiyya bai amfanar da al’ummar Najeriya da komai ba, face handama da kuma kama karya daga bangaren ‘yan siyasar kasar.
Attahiru Jega wanda kuma tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano ne, ya ce; al’ummar Najeriya basu ci gajiyar siyasar kasar ba sakamakon kama karyar ‘yan siyasa wanda ya alakanta da tasirin mulkin soji.
Tsohon shugaban na INEC ya bayyana hakan ne yayin wani taron kan cika shekaru 30 da dorewar mulkin dimukuradiya a nahiyar afurka wanda cibiyar dimukuradiya da ci gabanta ta shirya aka kuma gudanar Juma’ar nan a Abuja.
Ya ce mulkin dimukuradiyya ya samu gindi zama a nahiyar afurka, sai dai har zuwa yanzu wasu na ganin akwai sauran Rina a Kaba, inda masana ke aza ayar tambayar cewa ko mulkin dimukuradiyyar ya haifar da Da mai ido ko-ko a,a.
Farfesa Attahiru Jega ya kara da cewa, abin takaici shine yadda mulkin dimukuradiyar maimakon ya kawo sassautawar lamura, sai ya zama wani kafa na shimfida mulkin kama karya da kuma janyo hargitsi a nahiyar Afurka.