Kiwon Lafiya
Yan kasar biyu ne zasu wakilci Najeriya a gasar karatun alkur’ani ta duniya a bana
Yan najeriya biyu ne da suka yi nasara a gasar karatun alkur’ani mai girma a bana za su wakilci kasar nan a gasar karatun alkur’ani ta duniya da za ta ta gudana a watan Mayu a kasar Turkiyya.
Matasan makarantan biyu sun hadar da Abdurrahman Bunu daga jihar Borno sai kuma Yusuf Yahya daga jihar Edo.
Haka kuma za su halarci gasar ta duniya ne bayan da suka samu nasara a gasar kasa da aka gudanar a birnin tarayya Abuja da kungiyar bunkasa addinin musulunici ta IPIN da kuma kasar Turkiyya suka shirya aka kammala a juma’ar da ta gabata.
Abdurrahman Bunu daga jihar Borno shi ne yazo na daya a izu sittin da tafsiri inda Isma’il yazo na biyu daga jihar Neja sai kuma Abdulmalik Ahmad yazo na uku daga jihar Ogun.
Sai kuma a bangaren izu sittin da tangimi Yusif Yashua yazo na daya yayin da Ibrahim M Ibrahim daga jihar Borno ya zo na biyu sai kuma Ajmul Nura Shema daga jihar Katsina ya zo na uku.
A bangaren mata kuma Maimuna Abdurrahman daga yankin Abaji a birnin tarayya Abuja ta yi na daya a izu biyar, Aisha Sani daga Kuje ta yi na daya a izu goma da sauran mata da suka samu nasara a izu daban daban.