Connect with us

Labarai

Za a janye ‘yan sandan dake aiki a EFCC

Published

on

Babban sufeton ‘yan sandan kasar nan Muhammad Adamu ya bada umarnin janye dukannin ‘yan sandan da ke aiki a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da aka aikewa da mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda da kuma ‘yan sandan kwantar da tarzoma da sauran su, ana kuma basu umarnin su janye dukannin ‘yan sandan da ke aiki a hukumar ta EFCC.

Umarnin ya kuma tafi ne da kunshin hana duk wani mutum shiga harabar hukumar ta EFCC banda ma’aikatan ta, kuma ya zama wajibi ‘yan sandan da ke aiki a hukumar su koma shalkwatar rundunar da ke birnin tarayya Abuja da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin mai zuwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!