Labarai
‘Yan Nigeria 13, 235 aka koro su daga kasashen waje cikin shekaru 4 da suka gabata
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya gano cewa, akalla ‘yan Nigeria mazauna ketare dubu goma sha uku da dari biyu da talatin da biyar ne aka kora su daga kasashen da su ke zaune zuwa nan gida Nigeria, cikin shekaru hudu da suka gabata.
A cewar binciken an sallamo ‘yan Najeriyar ne daga kasashe goma da suka hada da: Libya, Mali, Burkina faso, Ghana, Afurka ta kudu da kuma Kamaru.
Sauran sune kasashen Saudi Arabia, Lebanon, Oman, sai kuma wadanda aka koro su daga cikin kasashe da ke kungiyar tarayyar turai.
Bugu da kari, binciken ya gano cewa mafi yawa na wadanda aka koro din, sun aikata laifuka ne da suka hada: shiga kasa ba bisa ka’ida ba, ko kuma wadanda suka aikata manyan laifuka da kuma wadanda takardun shaidar zamansu suka kare.
Rahotanni sun ce, kaso tamanin cikin dari na ‘yan Nigeria mazauna ketaren da aka koro, wato dubu tara da dari bakwai da hamsin da tara an taso keyarsu ne daga kasar Libya.
You must be logged in to post a comment Login