Connect with us

Labarai

Yan sanda 5,000 za su yi Ritaya a bana

Published

on

Rundunar ’yan sandan Najeriya, ta ce, akalla Jami’anta kimanin dubu biyar ne za su yi ritaya a shekarar nan da muke ciki.

 

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da fansho DCP Sani Doki Yusuf ne ya bayyana hakan a zantarsa da manema labarai a yayin horaswa na yankin Arewa maso Yamma ga jami’an da ke shirin yin ritaya.

 

A cewar DCP, an wayar da kan jami;an yan sandan kan muhimmancin cika takardun fansho yadda ya kamata domin kauce wa jinkiri wajen biyan haƙƙoƙi bayan ajiye aiki.

 

Ya na mai cewa, matsalolin da ake fuskanta a biyan fansho sun fi shafar kurakurai a bayanan sirri, musamman bambancin suna da rashin daidaiton takardu.

 

Ya kuma ce, rundunar ta sha alwashin ci gaba da kai ziyara rundunoni domin gyara irin waɗannan matsaloli ga jami’an da zasu yi ritaya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!