Labarai
‘Yan sanda a jihar Kwara sun hallaka ‘yan bidiga bayan yunkurin kai hari

Rundunar ’yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da kashe ’yan bindiga mutum biyu a harin da suka kai garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a ranar Talata. Harin ya tayar da hankula a yankin, inda mazauna yankin suka tabbatar da jin ƙarar harbe-harben maharan.
Sai dai an sha rabuwar kai tsakanin rahotanni dake fitowa dangane da harin, inda Wasu rahotanni suka nuna cewa maharan sun yi niyyar kai hari kan wata coci, yayin da wasu kuma suka ce sun shigo ne domin garkuwa da mutane kamar yadda suke yi a kai a kai.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi tayi ta tabbatar da cewa mutum biyu sun mutu a harin, yayin da ɗan kungiyar sa-kai guda ya jikkata.
You must be logged in to post a comment Login