Labaran Kano
‘Yan sanda sun baiwa ‘yan social media horo na musamman
Rundunar ‘yan sanda jihar Kano tare da hadin gwiwar gidauniyar inganta ayyukan jami’an tsaro NPP yanzu haka suna gabatar da taron wayar da kan ga mata ‘yan gwagwarmaya a shafukan sada zumunta na Internet.
Taron wanda yake gudana a yau Laraba a birnin Kano, ya samu halartar masu amfani da kafafan sada zumunta daga bangarorin siyasa daban-daban da addinai na jihar Kano da sauran matasa masu amfani da shafukan sada zumunta.
Kakakin rundunar ‘yan santa ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kyawa ya ce makasudun taron shi ne don kauda kalaman bantaci da labarun karya ta kafafan sada zumunta na Internet.
Daga cikin wadanda suka gabatar da mukala da takardu a yayin taron sun hadar da Malam Ali Isah wanda yayi bayani kan kafafan sada zumunta.
Yansanda sun cafke wata mata da tura kishiyar ta rijiya a karamar hukumar Rano
Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta ja hankali alumma kan zaben ranar Asabar
Masu kwacen waya sun zo hannu -‘Yan sanda
Sai kuma Basheer Sharfadi na Freedom Radio wanda ya gabatar da takarda kan labaran karya da kalaman batanci a kafafan sada zumunta da hanyoyin magance su.
Sauran wadanda suka gabatar da mukalun sun hadar da jami’in rundunar ‘yan sanda ta Kano ASP, Yusuf Isah ya gabatar da makala kan gudummuwar da ake tsammanin ‘yan social media zasu gudanar ta hannun jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.
Yayin da ASP, Adamu M. Muhammad ya gabatar da takardar sa akan irin abubuwan da ka iya zamowa laifi a kafafan na sada zumunta.
Shima a nasa jawabin kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Kano CP. Habu Ahmed Sani ya ja hankalin matasan da suka amfana da samun horo da su gujewa aikata duk wani abu da zai iya kawo tarzoma a a kafafan sada zumunta, a maimakon hakan ya roki matasan da su maida hankali kan rubutukan da zasu kawo hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.