Labarai
Yan sanda sun cafke mutane 27 da ake zargi da kashe soja a Kaduna
Ƴan sanda a jihar Kaduna sun ce sun kama mutum 27 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daba-daban.
Wata sanarwar da mai magana da yawun ƴansandan jihar DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce an samu nasarar kama ɓata-garin ne bayan wani samame da ta kai maɓoyarsu a yankin Kawo.
Ya ce cikin makaman da suka ƙwato sun haɗa da wuƙaƙe da adduna da fartanyu da kuma ƙunshin ganyayyaki da ake kyautata zaton tabar wiwi ce da kuma sauran kayan maye.
Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Rabiu Muhammad ya ƙara nanata ƙoƙarin rundunar wajen ganin an mutunta doka da oda a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa Kaduna jiha ce mai zaman lafiya, don haka ba za a bari wasu ɓata-gari ko masu son aikata laifi su wargaza zaman lafiyar jihar ba.
Ya kuma gargaɗi duk masu son tayar da hankali da su guji yin haka ko kuma su fice daga jihar, saboda ƴansanda za su ci gaba da farautarsu ko ina suka shiga a faɗin jihar.
You must be logged in to post a comment Login