Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kashe dan Sanata Na-Allah a Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da kisan Abdulkarim Na-Allah, babban da ga Sanata Bala Ibn Na’Allah.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Laraba.

Tun a ranar 29 ga watan da ya gabata ne Agusta, jami’an tsaro suka tabbatar mutuwarsa lokacin da aka tsinci gawarsa a dakinsa da ke Malali a Kaduna.

Jalige ya kara da cewa ana ci gaba da bincike don gano musabbabin kisan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!