Ƙetare
Yan tawayen M23 na ci gaba da tilastawa fararen hula tserewa daga Gabashin Congo

Harin ‘yan tawayen M23 na ci gaba da tilastawa fararen hula tserewa daga Gabashin Jamhuriyar Dumokaradiyyar Congo da birnin Sake da ke Gabashin kasar ke ci gaba da kasancewa cikin tashin hankali da fargaba sakamakon rikicin dake faruwa tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawaye.
Birnin ya kasance wata babbar cibya mai mahimmanci wajen kare birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Rahotanni daga ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama sun nuna cewa ‘yan tawayen M23 sun tilastawa dubban mutane barin gidajensu a garin Sake, inda aka kora su zuwa birnin Goma.
Duk da cewa an ƙulla yarjejeniyoyin tsagaita wuta tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen a kasashen Qatar da Amurka, faɗan ya ci gaba da ƙazanta tare da amfani da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuka kan fararen hula.
Rikicin ya tilastawa miliyoyin mutane barin muhallan su a sassan gabashin Congo, inda mutane da dama ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira cikin mawuyacin hali.
You must be logged in to post a comment Login