Ƙetare
Zan duba yuwuwar yin sulhu da Iran – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai duba sabon tayin sulhu da Iran ta gabatar, amma ya nuna shakku cewa Amurka za ta amince da shi. Ya ce Iran ba ta biya “farashi mai tsanani” ba kan abubuwan da ya zarge ta da aikatawa a duniya, don haka tayin na iya zama ba abin karɓa ba.
Tattaunawar sulhu tsakanin ƙasashen biyu ta tsaya cik tun bayan tsagaita wuta da aka yi a ranar 8 ga Afrilu, bayan yunkurin zaman sulhu da aka yi a Pakistan ya gaza. Rahotanni sun ce Iran ta gabatar da shirin maki 14, ciki har da kawo karshen rikici da kuma sabon tsarin kula da mashigar Hormuz mai muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
Trump ya kuma bar ƙofa a buɗe kan yiwuwar sake kai hare-hare idan Iran ta “yi wani abu mara kyau.” A gefe guda, jami’an Iran sun ce suna shirye su ci gaba da tattaunawa ko kuma su fuskanci gaba da gaba, suna zargin Amurka da rashin cika alkawura.
Rikicin ya haifar da matsin tattalin arziki, inda farashin mai ya tashi sosai, sannan Iran na fuskantar hauhawar farashi mai tsanani. Har ila yau, ana ci gaba da faɗa a yankin Lebanon tsakanin Isra’ila da Hezbollah, lamarin da ke ƙara dagula halin da ake ciki a yankin.
You must be logged in to post a comment Login