Labaran Wasanni
‘Yan wasan Najeriya na amfani da kwayoyin kara kuzari – Femi
Wani kwararre a masu yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari a harkokin wasanni, Mista Femi Ayorinde, ya ce an samu ‘yan wasan kasar nan guda shidda a bangaran guje-guje da tsalle-tsalle ‘yan kasa da shekara 14 da laifin amfani da kwayoyin kara kuzari a gasar wasannin matasa ta shekarar 2019 da aka gudanar a jihar Kwara.
Ayorinde ya bayyana haka ne a wata takarda da ya gabatar yayin wani taro na kwanaki biyu da kwamitin yaki da hana amfani da kwayoyin kara kuzari na kasa ya shirya ta kafar Internet, domin wayar da kan ‘yan wasan kasar nan.
An dai gudanar da taron ne cikin ranakun Juma’a da Asabar, inda ya samu halarta manyan kungiyoyin wasanni daban-daban sama da 300.
Ayorinde ya kara da cewa, lallai akwai matsala babba a harkokin wasanni a kasar nan, duba da yadda yara ‘yan kasa da shekara 14 suka fara amfani da kwayoyin kara kuzarin.
Haka kuma, shima wani Farfesa masani kan halayyar ‘yan wasa dake a jami’ar Ibadan, Olufemi Adegbesan, ta gargadi masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni na makarantu da su mayar da hankali wajen dogaro ga ‘yan wasan da suke da kwarewa ba ta hanyar amfani da kwayoyi ba, domin ganin an dakile yawaitar amfani da kwayoyin a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login