Labarai
Yankin arewa zai iya haramta sana’ar sayar da kayan gyara – malami ga gwamnonin kudu
Atoni janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya caccaki gwamnonin kudancin kasar nan sakamakon matakin da suka dauka na haramta kiwo a yankinsu.
A cewar Abubakar Malami haramta kiwo ga makiyaya a kudancin Najeriya dai-dai ya ke da gwamnonin arewa su haramta sana’ar sayar da kayan gyara kasancewar al’ummar kudanci sune mafi yawa da ke gudanar da sana’ar sayar da kayan gyaran a arewa
Ministan na shari’a ya bayyana hakan ne ta cikin shirin siyasa na Politics Today a gidan talabijin na Channels.
Atoni janar na tarayyar ya bayyana matakin da gwmanonin na kudanci suka dauka da cewa haramun ne don kuwa ya sabawa doka.
A makon jiya ne bayan kammala wani taro da suka gudanar a garin Asaba na jihar Delta gwamnonin kudancin Najeriyar goma sha bakwai ta cikin wata takardar bayan taro da suka fitar suka bayyana haramta yin kiwo barkatai a yankinsu.
You must be logged in to post a comment Login