Connect with us

Kaduna

Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun kashe ɗan majalisa a jihar Kaduna

Published

on

Ƴan bindiga sun kashe ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Giwa a majalisar dokokin jihar Kaduna Aminu Rilwan Gadagau.

Ɗan majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin ƙananan hukumomi da raya karkara na majalisar.

Sanata Shehu Sani ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na Twitter a ranar Laraba.

Cikin rubutun nasa, Sanata Shehu Sani ya ce, ƴan bindigar sun kashe shi ne a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

Ƙarin bayani zai zo muku anan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!